Shugaba Tinubu Ya Amince da Kafa Sababbin Jami'o'i 11 a Najeriya, An Jero Sunayensu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
State House, Abuja - Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta amince da ƙirƙiro sababbin jami'o' 11 masu zaman kansu ma'ana na kudi a faɗin ƙasar nan.
Gwamnatin karƙashin jagorancin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ta ba sababbin jami'o'in na kudi lasisin wucin gadi domin su fara aiki a Najeriya.

Asali: Facebook
Kamar yadda Leadership ta ruwaito, gwamnatin Najeriya ta ba jami'o'in damar fara aiki ne a wani yunkuri na bunƙasa harkokin ilimi da faɗaɗa damar shiga jami'o'i.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Ministan Ilimi na Tarayya, Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) a fadar shugaban kasa da ke Abuja
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ne ya jagoranci taron FEC a Aso Villa yau Litinin, 3 ga watan Maris, 2025 daidai da 3 ga watan Ramadan, 1446H.
1. New City University, Ayetoro – Jihar Ogun
2. University of Fortune, Igbotako – Jihar Ondo
3. Eranova University, Mabushi – Abuja, FCT
4. Minaret University, Ikirun – Jihar Osun
5. Abubakar Toyin University, Oke-Agba – Jihar Kwara
6. Southern Atlantic University, Uyo – Jihar Akwa Ibom
7. Lens University, Ilemona – Jihar Kwara
8. Monarch University, Iyesi-Ota – Jihar Ogun
9. Tonnie Iredia University of Communication, Benin City – Jihar Edo
10. Isaac Balami University of Aeronautics and Management, Lagos – Jihar Lagos
11. Kevin Eze University, Mgbowo – Jihar Enugu
A cewar Ministan Ilimi, amincewa da wadannan jami’o’i abu ne mai matukar muhimmanci domin kara habaka damar samun ingantaccen ilimi a Najeriya.
Tunji Alausa ya kara da cewa:
"Shugaba Bola Tinubu na da burin ganin an inganta harkar ilimi a kasar nan. Wannan matakin zai taimaka wajen rage cunkoso a jami’o’in gwamnati da kuma samar da karin guraben karatu ga matasa."
Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarin ci gaba da karfafa duk wani yunkuri na habaka ilimi.
Ta kuma sha alwashin tabbatar da cewa wadannan sababbin jami’o’i sun cika duk ka’idojin da hukumar kula da jami’o’i (NUC) ta gindaya, Tribune ta ruwaito.
Wannan mataki ya sa a yanzu Najeriya na da jami'o'i sama da 150 a faɗin jihohi 36 da Abuja kuma galibinsu na kudi ne.
A wani labarin, kun ji cewa Mai girma Bola Tinubu ya amince da kafa sababbin jami'o'in tarayya guda biyu a Najeriya domin bunkasa harkokin ilimi.
Jami’o’in da aka kafa sun hada da Jami’ar Fasaha da Kimiyyar Muhalli, Iyin Ekiti da Jami’ar Noma da Nazarin Ci Gaba, Iragbiji, Osun.
Asali: Legit.ng