Navigation

© Zeal News Africa

ADC: Shafin Hadakarsu Atiku Ya Samu Matsala sau 3 a Mako 1, An Bayyana Dalili

Published 2 days ago3 minute read

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

- Jam’iyyar ADC ta bayyana cewa shafinta na yanar gizo ya samu matsala sau uku a makon da ya gabata sakamakon yawan jama’ar da ke kokarin yin rajistar zama mambobinta.

Shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar (BoT), Ibrahim Mani, ne ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a ranar Litinin.

Jam'iyyar ADC ta ce shafinta na yanar gizo ya samu matsala sau 3 saboda yawan jama'ar da ke son rajista
Alhaji Atiku Abubakar yana raha da jiga-jigan adawa yayin da suka kaddamar da jam'iyyar ADC a Abuja. Hoto: @ADCYCC, adc.org.ng
Asali: UGC

Yayin tattaunawa da Channels TV, Ibrahim Mani ya ce yawan masu ziyartar shafin ya fi karfin tsarin da yake dauke da shi, lamarin da ya janyo ya samu matsala sau uku.

“Mun dauki matakin sauya shafin yanar gizonmu sau uku a cikin mako guda saboda tururuwar masu son yin rajistar zama ’yan jam’iyyar ta hanyar intanet,”

- Inji Ibrahim Mani.

Legit Hausa ta fahimci cewa karuwar yawan masu ziyartar shafin ta biyo bayan bayyana ADC a matsayin sabuwar jam'iyyar hadakar ’yan adawa a Najeriya.

Fitattun jiga-jigan ’yan adawa ciki har da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na LP a 2023 Peter Obi, tsohon shugaban majalisar dattawa David Mark, da tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola sun shiga jam'iyyar.

Ibrahim Mani ya jaddada kudurin jam’iyyar na gina babban dandalin ’yan adawa a kasar, tare da karbar sababbin mambobi da suka dace da manufofin ADC.

“Jam’iyyar siyasa gida ce ga kowa. Ba za a ce an ware wani mutum ba matukar ba wai kotu ta taba kama shi da aikata wani laifi ba.
"Domin kundin tsarin mulki ya haramta wa wanda kotu ta yankewa hukunci kan wani laifi shiga jam’iyya domin ya tsayawa takara."

- Ibrahim Mani.

Jam'iyyar ADC na fatan zama babbar jam'iyyar 'yan adawa da kuma lashe zabe a 2027
Jam'iyyar ADC ta yi karfi bayan Atiku, El-Rufai, Peter Obi sun kaddamar da ita a Abuja. Hoto: @ADCYCC
Asali: Twitter

Jam'iyyar ADC na kokarin zama madadin jam’iyyun da ke da rinjaye a kasar ta hanyar hadin gwiwa da jiga-jigan 'yan Najeriya da kuma karfafa siyasa daga tushe.

Ibrahim Mani ya ce ’yan Najeriya na neman sauyi mai ma’ana musamman a wannan lokaci da ake fama da matsin tattalin arziki, wanda hakan ke karfafa sha’awa ga shiga jam’iyyar.

“Ya fi kyau a gina jam’iyyar da mutane masu kishin samar da sahihiyar adawa za su so shigarta fiye da barin Najeriya ta koma jam’iyya guda daya,” inji Ibrahim Mani.

Ya kuma ce jam’iyyar ADC na kokarin dawo da ayyuka zuwa yanar gizo yayin da ake ci gaba da wayar da kai ta hanyar tuntuɓar jama’a kai tsaye.

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Adamu Waziri, ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa PDP kuma mamba a kwamitin amintattu (BoT), ya fice daga jam’iyyar, ya koma ADC.

Ya ce matakin ya biyo bayan damuwarsa kan halin ƙuncin da ’yan Najeriya ke ciki da kuma gazawar PDP wajen zama sahihiyar jam’iyyar adawa.

Waziri ya bayyana cewa ADC na da ƙarfin da za ta iya karɓe mulki daga hannun APC a 2027 domin dawo da martabar tattalin arziƙin ƙasa.

Asali: Legit.ng

Origin:
publisher logo
LegitNg
Loading...
Loading...
Loading...

You may also like...