Navigation

© Zeal News Africa

Hadimin Tinubu Ya Fadi Damar da Atiku Ya Rasa Ta Zama Shugaban Kasa

Published 2 days ago3 minute read

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Hadimin shugaban ƙasa, Daniel Bwala, ya yi magana kan tsohon ubangidansa, Atiku Abubakar.

Daniel Bwala ya bayyana cewa wataƙila tsohon mataimakin shugaban ƙasan ba zai taɓa zama shugaban Najeriya ba duk da shekarun da ya shafe yana fafutukar neman kujerar.

Bwala ya yi magana kan Atiku
Daniel Bwala ya ce watakila Atiku ba zai zama shugaban kasa ba Hoto: @Danielbwala, @atiku
Asali: Twitter

Daniel Bwala ya bayyana hakan ne lokacin da yake magana a cikin shirin 'Politics Today' na tashar Channels Tv.

Bwala wanda ya kasance mai magana da yawun Atiku a lokacin zaɓen 2023, ya ce da alama Atiku ya gama amfani da duk damar da zai iya samu don cimma burinsa na zama shugaban ƙasa.

"Bisa gaskiya, na bayyana ra’ayina cewa wataƙila Allah bai kaddara masa zama shugaban Najeriya ba, domin ya yi duk abin da ya kamata a yi amma bai lashe zaɓen shugaban ƙasa ba.”
“Shekarar 2023 ita ce babbar damar da tsohon ubangidana Atiku Abubakar ya samu. Ba zai sake samun irin wannan damar ba."

- Daniel Bwala

Bwala ya kuma yi fatali da yiwuwar nasarar sabuwar haɗakar jam’iyyun adawa da suka haɗa da ɗan takarar jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi, da kuma tsohon jigo a APC, Rotimi Amaechi, wajen kayar da Shugaba Bola Tinubu a 2027.

Ya soki yadda ƙawancen ya zaɓi jam’iyyar ADC a matsayin dandalin siyasarsu, yana cewa babu wasu kwararan manufofi ko tsari na daban da suke fitarwa.

“Abin da har yanzu ke ba ni mamaki shi ne, wannan haɗakar ta ƴan siyasar da suka rasa matsuguni ba su da ƙarfin gwiwar fitar da manufofi da suka bambanta ko shirye-shirye na yin gyara."

- Daniel Bwala

Daniel Bwala ya yi magana kan Atiku
Bwala ya ce hadaka za ta wargaje Hoto: @atiku
Asali: Facebook

Daniel Bwala ya kuma yi hasashen cewa haɗakar za ta rushe cikin watanni shida saboda rikicin ƙarfi da iko dangane da wanda zai zama ɗan takarar shugaban ƙasa daga cikinsu.

Ya ambaci wata magana da Datti Baba-Ahmed ya yi, inda ya bayyana cewa babbar barazana ga haɗin kan haɗakar ita ce burin da kowane daga cikinsu ke da shi na son zama shugaban ƙasa.

“Ɗaya daga cikinsu, sunansa Datti (Baba-Ahmed), ya riga ya hango haɗarin da ke gabansu. Ya ce matsalar wannan haɗaka ita ce wanda zai zama shugaban ƙasa, domin a cewarsa, ‘kowa yana so ya zama shugaban ƙasa’."

- Daniel Bwala

A wani labarin kuma, kun ji cewa abokin takarar Peter Obi a zaɓen 2023, Yusuf Datti Baba-Ahmed ya ba jam'iyyar ADC shawara.

Datti Baba-Ahmed ya buƙaci jam'iyyar ADC da ka da ta yi kuskuren ba da tikitin takararta ga Alhaji Atiku Abubakar.

Tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasan ya bayyana cewa idan aka ba Atiku takara, cikin sauƙi jam'iyyar APC za ta kayar da shi.

Asali: Legit.ng

Origin:
publisher logo
LegitNg
Loading...
Loading...
Loading...

You may also like...