Tinubu Ya Rufe Bakin Ƴan Adawa, Ya Faɗi abin da ake Yi da Kudin Tallafin Man Fetur
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
- Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yi amfani da kuɗaɗen da aka samu daga cire tallafin fetur wajen gina manyan ababen more rayuwa a faɗin ƙasar.
Tinubu ya bayyana hakan ne a taron ƙasa kan asusun gwamnati da tsarin kula da kuɗaɗe da aka shirya a Abuja, karkashin jagorancin kwamitocin kula da asusun gwamnati na majalisar dattawa da ta wakilai.

Asali: Facebook
Ministar harkokin kuɗi ta ƙasa, Doris Nkiruka Uzoka-Anite ce ta wakilci shugaban a taron, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.
Rahoton ya nuna cewa taken taron shine: “Gudanar da kuɗi a Najeriya: Samar da sabuwar hanyar riko da gaskiya da ci gaba mai dorewa."
Taron ya ba shugaba Tinubu damar bayyana yadda aka karkatar da kuɗin tallafi zuwa ga shirye-shiryen tallafa wa marasa ƙarfi da gyare-gyaren tattalin arziƙi.
A cewar shugaban kasar, wadannan ayyukan da ake yi da kudaden da ake samu daga tallafin yana taimakawa wajen gina amana tsakanin gwamnati da al'umma da ci gaba mai ɗorewa.
Shugaban ya ce akwai raɗaɗi a cire tallafin fetur, ya ce yin hakan wajibi ne domin buɗe damarmaki na kuɗi da karkatar da albarkatun ƙasa zuwa sassan da ke amfani ga mafi yawan al’umma.
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya shawarci kwamitocin kula da asusun gwamnati da su yi amfani da ikon kundin tsarin mulki wajen tabbatar da gaskiya da rikon amana a harkokin gwamnati.
Sanata Abdul Ningi ne ya wakilce shi a taron, inda ya yi gargaɗi kan yadda hukumomi ke ƙin amsa gayyatar majalisa, yana mai cewa hakan na zama barazana ga tsarin doka, inji rahoton NTA News.
Shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, wanda shugaban masu rinjaye Julius Ihonvbere ya wakilta, ya bayyana damuwa kan batutuwan da ba a warware ba dangane da asusun gwamnati.
Tajudeen Abbas ya bayyana cewa sama da Naira biliyan 300 na kuɗaɗen jama’a ne rahotannin bincike suka nuna ba su koma hannun gwamnati ba har yanzu.

Asali: Twitter
Shugaban kwamitin kula da asusun gwamnati na majalisar wakilai, Bamidele Salam, da takwaransa na majalisar dattawa, Ahmed Wadada, sun bukaci a sake fasalin tsarin gudanar da kuɗin gwamnati a Najeriya.
Sun bukaci jami’an gwamnati su daina magana kawai, su tabbatar da cewa kuɗin jama’a na zuwa inda ya kamata domin amfanin al’umma.
Dukkaninsu sun jaddada cewa ya kamata taron ya haifar da sakamakon da za a iya aunawa a ma'auni, kuma a tabbatar ya shafi rayuwar 'yan Najeriya kai tsaye.
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya kaddamar a muhimman gine-ginen ababen more rayuwa a Legas da babban birnin tarayya Abuja.
A lokacin da yake hutu a Legas, Shugaba Tinubu ya kaddamar da wasu muhimman ayyuka, ciki har da babban titin gabar teku na Legas zuwa Calabar.
A Abuja kuwa, Tinubu ya kaddamar da ginin cibiyar taruka ta kasa (ICC), ɗaya daga cikin ayyuka 17 da Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya kammala.
Asali: Legit.ng
You may also like...
Diddy's Legal Troubles & Racketeering Trial

Music mogul Sean 'Diddy' Combs was acquitted of sex trafficking and racketeering charges but convicted on transportation...
Thomas Partey Facing Rape & Sexual Assault Charges

Former Arsenal midfielder Thomas Partey has been formally charged with multiple counts of rape and sexual assault by UK ...
Nigerian University Admission Policy Changes

JAMB has clarified its admission policies, rectifying a student's status, reiterating the necessity of its Central Admis...
Ghana's Economic Reforms & Gold Sector Initiatives

Ghana is undertaking a comprehensive economic overhaul with President John Dramani Mahama's 24-Hour Economy and Accelera...
WAFCON 2024 African Women's Football Tournament

The 2024 Women's Africa Cup of Nations opened with thrilling matches, seeing Nigeria's Super Falcons secure a dominant 3...
Emergence & Dynamics of Nigeria's ADC Coalition

A new opposition coalition, led by the African Democratic Congress (ADC), is emerging to challenge President Bola Ahmed ...
Demise of Olubadan of Ibadanland

Oba Owolabi Olakulehin, the 43rd Olubadan of Ibadanland, has died at 90, concluding a life of distinguished service in t...
Death of Nigerian Goalkeeping Legend Peter Rufai

Nigerian football mourns the death of legendary Super Eagles goalkeeper Peter Rufai, who passed away at 61. Known as 'Do...