Liverpool da Madrid na gogayya kan Wirtz, Rashford ya gana da shugabannin Barca - BBC News Hausa
Asalin hoton, Getty Images
Liverpool da Real Madrid na gogayya kan kan dan wasan Bayer Leverkusen Florian Wirtz, Arsenal ta bayyana kudin sayen dan wasan gaba na RB Leipzig Benjamin Sesko, yayin da Manchester United da Chelsea ke neman dan wasan gaban Ipswich Liam Delap.
Real Madrid na yunkurin dauko dan wasan Bayer Leverkusen Florian Wirtz duk da cewa dan wasan na Jamus mai shekara 22 yana da ra'ayin komawa Liverpool. (AS Spanish)
Brentford ta tuntubi Liverpool kan sayen golan Jamhuriyar Ireland Caoimhin Kelleher, mai shekara 26, kan fam miliyan 20. (Liverpool Echo)
Yunkurin na daukar Kelleher ya zo ne a daidai lokacin da Brentford ke shirin barin golan Holland mai shekara 31 Mark Flekken ya koma Bayer Leverkusen. (Independent)
Bayern Munich na sha'awar sayen dan wasan gaban Liverpool Cody Gakpo, mai shekara 26, inda kulob din Bundesliga ke daya daga cikin kungiyoyi uku da dan kasar Netherlands din ke son komawa. (Florian Plettenberg)
Skip Wanda aka fi karantawa and continue reading
End of Wanda aka fi karantawa
Dan wasan baya na Bournemouth Milos Kerkez ya riga ya amince ya koma Liverpool kuma babu wata damuwa da ta rage. (Fabrizio Romano)
Wakilin dan wasan gaba na Manchester United Marcus Rashford ya gana da daraktan wasanni na Barcelona Deco, dan kasar Ingilan mai shekaru 27, yana da burin komawa gasar La Liga. (Sports)
Arsenal na zawarcin dan wasan Jamus Leroy Sane, mai shekara 29, wanda kwantiraginsa zai kare a Bayern Munich a wannan bazarar. (Times)
Newcastle na daya daga cikin kungiyoyin da ke kokarin kulla yarjejeniya da dan wasan gaban Ipswich Town Liam Delap, mai shekara 22, wanda kuma ke samun tayi daga Chelsea, Manchester United da Everton. (ipaper)
RB Leipzig ta shaida wa Arsenal cewa dole ne ta biya fam miliyan 92.5 don siyan dan wasan gaban Slovenia Benjamin Sesko, mai shekara 21, wanda itama Manchester United ke zawarcinsa.
Dan wasan tsakiya na Ingila Jordan Henderson, mai shekara 34, zai iya barin kulob din Ajax na Holland ya koma kulob din Sunderland na gida a bazara. (Mirror)
Zakarun Italiya Napoli na shirin kulla yarjejeniya da dan wasan tsakiya na Belgium Kevin de Bruyne, mai shekara 33, da kuma dan wasan Canada Jonathan David, mai shekara 25, domin komawa kulob din na Seria A (Corriere dello Sport)
Roma na gab da nada Gian Piero Gasperini a matsayin sabon kocinta bayan da dan kasar Italiyan ya bar Atalanta bayan shekaru tara yana jan ragamar kungiyar. (Gazzetta dello Sport)