Karshen Alewa: Sojoji Sun Gano Maboyar Bello Turji a Zamfara, Sun Kaddamar da Hari
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
- Sojojin Operation Fansan Yamma sun samu nasarar tarwatsa maboyar fitaccen ɗan ta’adda, Bello Turji, a jihar Zamfara.
Wannan farmakin ya taimaka wajen gano manyan makamai, abin da ya zama matakin ci gaba a yaki da miyagun laifuffuka a yankin.

Asali: Twitter
Sojojin Fansan Yamma da ke karkashin Operation Tsatsa Daji III sun ƙara himma wajen kawar da sansanonin ‘yan ta’adda a Shinkafi da Zurmi, inji rahoton Zagazola.
: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Bayanan sirri sun tabbatar da cewa sojojin sun kai farmaki bayan samun bayanan sirri kan ‘yan ta’adda da suka sake taruwa a kauyen Katsira.
Sojojin ba su gano komai a binciken farko da suka gudanar ba, lamarin da ya sa suka kutsa cikin kauyen Fakai, sananniyar maboyar ‘yan ta’adda.
Sojojin sun tarwatsa Garin Fakai, wacce ta kasance maboyar Bello Turji, ɗaya daga cikin fitattun manyan ‘yan ta’adda a Najeriya.
Majiyoyin soja sun tabbatar da cewa an kona gine-ginen sansanin, yayin da ‘yan ta’adda suka tsere, suka bar mata da yara da ke tsare a hannunsu, waɗanda sojojin suka kubutar.
An rahoto cewa a yayin farmakin, sojojin sun gano bindigogi kirar AK47, bama-baman RPG da harsasai da dama.
A wani labarin, mun ruwaito cewa, rundunar soji, karkashin Operation Hadarin Daji, ta kara kaimi wajen farautar shugaban 'yan ta’adda, Bello Turji.
Wannan bayanin ya biyo bayan rade-radin da ake yi na cewa an cafke Bello Turji, lamarin da rundunar sojojin ta musanta a fili.
Sai dai rundunar sojin ta jaddada cewa ba za ta yi sako-sako ba, har sai an damƙe fitaccen ɗan ta’addan da ya addabi al’umma.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng